• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAN BINDIGA SUN KAI FARMAKI KAN OFISHIN DSS DA FRSC A NNEWI JIHAR ANAMBRA

‘Yan bindiga da ke cin Karen sub a babbaka a kudu maso gabashin Najeriya sun kai hari kan ofishin rundunar tsaron farin DSS da na jami’an kiyaye hatsari a garin Nnewi jihar Anambra.

Jaridar Dailry Trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun taho a manyan motoci 4 su ka yi harbin iska a wata magamar hanya daga nan su ka nufi ofisoshin biyu.

Akwai bayanai masu musanta juna da ke cewa an samu asarar ran mutum biyu da ke wucewa lokacin farmakin.
Daga bisani ‘yan bindigar sun bar wajen su ka nufi wani sasashen birnin, amma ba labarin sojojin da su ka bi su, sun tarar da su don ba a ji musayar wuta ba.

‘Yan sanda sun ce sun zagaye inda akasin ya auku.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *