• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN HARBE WANI MAI BABUR A JIHAR IMO YAYIN HARI A WATA KASUWA

‘Yan bindiga sun cigaba da zubar da jini a jihar Imo da Abia inda a yankin karamar hukumar Mbaitoli a jihar Abia su ka tunkari wata kasuwa su ka kashe wani mai tuka babur.

Miyagun irin sun zo ne a mota kirar sienna inda kuma su ka bude wuta a kokarin tafiya da mutumin da a ka gano sunan sa Chima.

Bayanai sun nuna wanda ya rasa ran na sa yaki amincewa ya shiga motar ‘yan ta’addan, don haka su ka harbe shi har lahira.

Harin ya auku ne daidai lokacin da babban sufeton ‘yan sanda Usman Baba Alkali ke gidan gwamnatin jihar a Owerri a ziyarar aiki.

Hakika wannan ya nuna yanda zubar da jini ya zama ruwan dare a wadannan jihohi biyu na kudu maso gabashin Najeriya

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN BINDIGA SUN HARBE WANI MAI BABUR A JIHAR IMO YAYIN HARI A WATA KASUWA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.