• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN HARBE JAMI’IN HUKUMAR NDLEA A JIHAR IBONYI

ByNoblen

Feb 21, 2022 ,

A cigaba da hallaka mutane don mugun nufi daga ‘yan bindiga a kudu maso gabashin Najeriya, ‘yan bindiga sun yi kisan gilla ga jami’in hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA.
Rahotanni sun baiyana cewa miyagun irin sun kai harin ne a madakatar binciken miyagun kwayoyi kan hanyar Enugu zuwa Abakaliki daf ga madakatar bincike ta sojoji.
An kai harin kan tawagar jami’an na NDLEA inda miyagun su ka harbi biyu daga jami’an da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya a ciki dayan kuma kafar sa ta karye.
Zuwa yanzu ba a baiyana sunayen wadanda lamarin ya rutsa da su ba kuma miyagun sun banka wuta ga motar sintiri ta jami’an na NDLEA.
Wannan harin ya biyo bayan wani irin sa da miyagun su ka kai har su ka yi kisan gilla ga jami’an ‘yan sanda.
Hakanan har ila yau harin ya zo ne ‘yan kwanaki kalilan bayan harin da ‘yan awaren Biyafara su ka kai kan kasuwar shanu ta Aba a jihar Abia su ka kashe ‘yan kasuwar shanu ‘yan arewa 8 da bindige shanu masu yawan gaske.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN BINDIGA SUN HARBE JAMI’IN HUKUMAR NDLEA A JIHAR IBONYI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.