• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN HARBE JAMI’AN TSARO BIYU A YENAGOA

‘Yan bindiga a babban birnin jihar Bayelsa wato Yenagoa sun harbe jami’an tsaro biyu da su ka hada da sajan na ‘yan sanda da kuma jami’in tsaron farar hula wato SIBIL DIFENS.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a Bayelsa Asinim Budtwat ya ce an yi kisan gilla ga jami’an biyu a kan wata magamar hanya yayin musayar wuta da ‘yan bindigar.

Hakanan Bustwat ya ce ‘yan bindigar sun sace mahaifin shugaban karamar hukumar Ogbia a jihar ta Bayelsa Gbalipre Turner.

Miyagun sun shiga gidan tsohon a Yenagoa su ka yi awun gaba da shi zuwa wani waje da ba a sani ba.

Bustwat ya ce ‘yan sandan sun yi wuf su ka bi miyagun har miyagun su ka watsar da motar su, su ka kuma arce da tsohon a wani karamin jirgin ruwa mai gudun tsiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI馃榾馃榾馃榾
One thought on “‘YAN BINDIGA SUN HARBE JAMI’AN TSARO BIYU A YENAGOA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *