• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN HALLAKA ‘YAN SANDA BIYU CIKIN MUTUM UKU A ANAMBRA

ByNoblen

Jul 17, 2022

‘Yan bindiga sun yi kisan gilla ga jami’an ‘yan sanda biyu cikin mutum uku da su ka yi wa kofar rago a karamar hukumar Awka ta kudu a jihar Anambra.
Jami’an ‘yan sandan na kan binciken gano wata motar safa ne da ‘yan bindigar su ka sace inda miyagun su ka kama ‘yan sanda biyu da kwarerre mai bin sawun motar sata; su ka kashe su da kona gawar su.
Kakakin ‘yan sanda a jihar Tochukwu Ikenga ya tabbatar da aukuwar akasin inda ya ce duk da haka ‘yan sandan sun hallaka wasu daga barayin yayin da wasu su ka tsere da raunukan harbin bindiga.
An gano kwarangwal na mutum da mota kirar siyasa a wajen ‘yan bindigar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN BINDIGA SUN HALLAKA ‘YAN SANDA BIYU CIKIN MUTUM UKU A ANAMBRA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.