‘Yan bindiga a jihar Anambra sun fille kan wani tsohon dan majalisa bayan sun yi ma sa kisan gilla.
Dan siyasar dai mai suna Nelson Achukwu ya samu iftila’in sace shi da ‘yan bindigar su ka yi da zargin sa cewa ya na samawa jami’an tsaro bayanai a kan ‘yan bindigar.
Da farko da a ka sace shi an sako shi don gano ba shi da laifi, amma daga bisani ‘yan bindigar sun sake sace shi inda su ka fille kan sa duk da iyalin sa sun biya diyyar Naira miliyan 15.
Zubar da jini a kudu maso gabashin Najeriya na kara zama ruwan dare.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀