• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN CIGABA DA MUGUN AIKI A YANKIN SABON BIRNI JIHAR SOKOTO

ByNoblen

Dec 13, 2021 ,

‘Yan bindiga ko a ce barayin daji na cigaba da kai hare-hare a yankunan karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto.
Rahotanni sun baiyana sace mutane a wasu kauyuka biyu na karamar hukumar inda har a ke fargabar mutum biyu sun rasa ran su.
Majiya daga shugaban rundunar adalci ta Sokoto Basharu Guyawa ta ce an ma sace limamin masallacin Izala na kauyen Gatawa Aminu Garba.
Wannan ya zo ne a tsaknain ziyarar babbar tawagar gwamnatin taraiya ta jami’an sirri jihar ta Sokoto don jajantawa da ba da kwarin guiwa.
Shugaba Buhari ya tura tawagar karkashin jagorancin mai taimaka ma sa kan tsaro Babagana Monguno inda ta gana da gwamna Aminu Tambuwal da nanata kudurin gwamnati na murkushe miyagun irin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN BINDIGA SUN CIGABA DA MUGUN AIKI A YANKIN SABON BIRNI JIHAR SOKOTO”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *