• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN BUGA NAKIYA A KATANGAR GIDAN YARIN ABOLONGO A OYO

Byadmin

Oct 24, 2021

‘Yan bindiga sun buga nakiya su ka zubar da katangar gidan yarin Abolongo da ke garin Oyo a jihar Oyo kudu maso yammacin Najeriya su ka sa masu jiran shari’a 837 su ka arce.

Miyagun dai ba su illata cikin gidan yarin ba amma sun zubar da Katanga ta inda masu jiran shari’ar su ka tsere.

Jami’in labaru na rundunar gidan yari a Oyo Olanrewaju Anjorin ya ce a cikin wadanda su ka arcen, an samu nasarar cafke 262 inda sauran 575 kuma ba a same su ba.

Rundunar gidan yarin ta ce ta dukufa wajen kamo dukkan masu jiran shari’ar da su ka gudu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN BINDIGA SUN BUGA NAKIYA A KATANGAR GIDAN YARIN ABOLONGO A OYO”

Leave a Reply

Your email address will not be published.