• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA SUN BUDE WUTA KAN TAWAGAR MATAFIYA A YANKIN KARAMAR HUKUMAR SABON BIRNI

Rahotanni daga jihar Sokoto na baiyana cewa ‘yan bindiga sun bude wuta kan wata motar safa dauke da fasinjoji 24 a yankin karamar hukumar Sabon Birni.
Zuwa yanzu dai labarin ya tabbatar da mutuwar mutum 5 inda wasu mutum 8 ke kwance a asibiti don jinyar kunar wuta.
Baya ga bude wuta kan motar, ‘yan bindigar sun cinna ma ta wuta da ya kawo samun kuna ga mutanen.
Wadanda ke cikin motar sun hada da maza da mata.
A na ganin ‘yan bindiga da ke gungun kasurgumin barawon daji Turji su ka aikata wannan mugun laifi.
 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.