• Fri. Sep 30th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAN BINDIGA A IMO SUN HALLAKA SARAKUNAN GARGAJIYA BIYU DA RAUNATA WASU

 

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wajen taron sarakunan gargajiya a jihar Imo inda su ka yi kisan gilla ga biyu daga cikin su.

Akasin ya auku ne a yankin karamar hukumar Njaba yayin sarakunan ke taro kuma hakan ya sa sarakunan sun fice daga wajen a firgice.

Baya ga rasa ran sarakuna biyu Eze E.A Durueburuo da Eze Sampson Osunwa, wasu daga sarakunan sun samu raunuka inda a ka garzaya da su asibiti.

Kakakin ‘yan sanda a jihar mai kalubalen ‘yan awaren Biyafara masu kashe mutane, Mike Abattam ya tabbatar aukuwar harin.

In za a tuna a nan jihar Imo ne ‘yan bindiga su ka yi kisan filla ga tsohon mai taimakawa shugaba Jonathan kan siyasa Alhaji Ahmed Gulak.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “YAN BINDIGA A IMO SUN HALLAKA SARAKUNAN GARGAJIYA BIYU DA RAUNATA WASU”

Leave a Reply

Your email address will not be published.