• Thu. Sep 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN AWAREN IPOB SUN KASHE DA FILLE KAN SOJOJI

Rundunar sojan Najeriya ta yi tir da kungiyar ‘yan awaren Biyafara ta IPOB don kashe da fille kan sojoji biyu a jihar Imo.

Miygaun irin sun tare soja mai suna Linus Audu da wacce ya ke shirin su yi aure da ita Gloria Matthew wacce ita ma soja ce, su ka kashe su da kuma fille kawunan su.

Gloria dai ‘yan jihar Imo ce daga karamar hukumar Nkwerre wacce ke tafiya gida da Linus don gabatar da shi ga iyaye a daura mu su auren gargajiya.

Kakakin rundunar sojan Onyema Nwachukwu ya ce ‘yan ta’addan da ke tutiyar kare al’ummar kudu maso gabar ba su duba ‘yar yankin su Gloria ba, su ka kashe ta da wanda ta ke kauna.

Nwachukwu ya ce wannan na nuna ‘yan IPOB ba muradun Igbo su ka karewa ba, ‘yan ta’adda ne kawai.

Rundunar ta yi matukar bacin cikin kisan gilla ga jami’an na ta biyu

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.