• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN APC SUN FUSATA SUN TARA TSINTSIYOYI HAR SUN KA KONA SU

ByYusuf Yau

Jun 20, 2021 , , , ,

Wasu ‘yan jam’iyyar APC mai mulki a Kwaea sun fusata da shugabannin jam’iyyar a jihar inda su ka tara curin tsuntsiya su ka banka mu su wuta don nuna bara’a ga jam’iyyar.

Fusatattun sun fito daga dukkan kananan humumomin jihar 16 su na masu zargin gwamnan jihar Abdulrahman Abdulrazak da nuna mu su wariya.

Tsohon mai neman tikitin takarar gwamnan jihar Yakubu Gobir ya jagoranci gangamin a babban birnin jihar Ilorin.
Masu boren sun ce jam’iyyar ta dau mataki da gangan na hana wasu damar sabunta rejistar jam’iyyar da a ka yi kwanan nan don neman ture su daga yin tasiri a zaben 2023.

A yanzu dai wadannan mutanen sun aiyana kafa wata sabuwar tafiya don sanin makomar su a siyasance.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *