• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAMANAWA SUN GIRGIZA DA KASHE YARINYA MAI SHEKARU 5 DA HOUTHI TA YI

ByNoblen

Jun 8, 2021 , , ,

Al’ummar Yaman sun girgiza ainun da harin ‘yan tawayen Houthi mabiya Shi’a su ka kai kan gidan mai a yankin Marib na tsakiyar kasar inda cikin wadanda su ka kashe har da yarinya mai shekaru 5. 

Ganin hoton yarinyar da mahaifin ta a kone ya haddasa suka mai zafi a ciki da wajen kasar inda a ka bukaci yin tir da ‘yan tawayen da kara sanya su a bakin littafin ‘yan ta’adda. 

Yarinyar mai suna Lian Taher na cikin motar mahaifin ta ne lokacin da ‘yan tawayen da Iran ke marawa baya su ka cillo makamin. 

Houthi na neman kwace Marib mai arzikin iskar gas daga hannun zababbiyar gwamnatin kasar ta Abed Rabbo.

Kazalika harin na makami mai linzami ya hallaka yaro mai shekaru 10 Hassan Al-Hubaishi. 

Kimanin mutum 21 su ka rasa ran su sanadiyyar mummunan harin inda gommai su ka samu raunuka. 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
41 thoughts on “YAMANAWA SUN GIRGIZA DA KASHE YARINYA MAI SHEKARU 5 DA HOUTHI TA YI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.