• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAMAN-TAWAGAR TARAIYAR TURAI A ADEN TA MARA BAYA GA KOKARIN GWAMNATIN ABED RABBO

Wakilan taraiyar turai da su ka shiga birnin Aden na kusancin Yaman sun nuna goyon baya ga yanda gwamnatin kasar ta Abed Rabbo kan yunkurin kawo zaman salama.

Birnin Aden ke zaman babban birnin wucin gadi na gwamnatin kasar don asalin birnin Sanaa na hannun ‘yan tawayen Houthi ‘yan shi’a.

Jami’an na turai na nuna ‘yan tawayen Houthi na kawo cikas a tattaunawar musayar fursunoni tsakanin su da gwamnati a birnin Amman.

Gwamnatin Yaman ta ce ‘yan Houthi sun kawo cikas na kin sako fursunoni ‘yan jarida, ‘yan gwagwarmaya da masu tsananin rashin lafiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.