• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAMAN: GWAMNATI DA ‘YAN TAWAYEN SUN YI MUSAYAR FURSUNONI

Gwamnatin Yaman ta shugaba Abed Rabbo Mansur Hadi da ‘yan tawayen Houthi ‘yan Shia da Iran ke marawa baya sun fara musayar daruruwan fursunoni.
Cikin wadanda Houthi ta sako har da Amurkawa biyu, ‘yan Saudi 15 da ‘yan Sudan 4.
Wadanda a ka saken sun sauka a Riyadh.
Sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya nuna farin ciki ga yunkurin na diflomasiyya da ya kai ga sakin Amurkawa biyu da ‘yan tawayen na houthi su ka kama.
Lamarin ‘yan tawayen houthi ya hana gwamnatin da duniya ta amince da ita aiki a Yaman inda ‘yan tawayen ke samun makamai daga Iran da hakan har ya kai su ga yin mummunan kisan gilla ga tsohon shugaban Yaman Ali Abdallah Saleh.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.