• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAMAN-BOM DIN MOTA YA YI SANADIYYAR MUTUWA MUTUM 6 A YAYIN AUNA GWAMNAN ADEN

ByHassan Goma

Oct 11, 2021 ,

 

Bom din mota a Yaman da ya tashi ya yi sanadiyyar mutuwar mutum mutum 6 a yayin da a ka auna harin kan gwamnan babban birnin gwamnatin kasar Aden na kudancin kasar.

Bom din ya tashi daidai lokacin da gwamnan Ahmad Hamed Lamlis da ministan noma Salem Al-Soqatri ke komawa gida daga wani aiki da su ka je a daidai anguwar Tawahi.

Tawahi anguwa ce da ke dauke da helkwatar ‘yan awaren kudancin Yaman amma kuma sun hada kai da gwamnati.

Allah ya tserar da rayuwar gwamnan amma jami’in labarum sa, mai dauka ma sa hoto da babban jami’in tsaron sun riga mu gidan gaskiya.

Shugaban kasar Abed Rabbo Mansur Hadi ya ba da umurnin nan ta ke a gudanar da bincike don cafko wadanda su ka kai harin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *