• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

‘YAN BINDIGA UKU SUN GAMU DA GAMON SU A ORLU IMO-‘YAN SANDA

Rundunar ‘yan sanda a jihar Imo ta ce ‘yan bindiga uku sun gamu da gamon su biyo bayan tinkarar ofishin rundunar a Orlu da miyagun irin dauke da makamai su ka yi.

‘Yan ta’addan sun bude wuta da jefa bom din kwalba kan ofishin ‘yan sandan har a ka samu gobara a rufin ofishin.

Sanadiyyar hakan ‘yan sanda su ka maida wuta har su ka yi nasarar hallaka uku daga miyagun inda sauran su ka arce daji da raunukan harbin albarusai.

An samu bindigogin wadanda a ka kashe inda yanzu a ke neman wadanda su ka arce musamman ta neman hadin kan asibitoci don ba da labarin duk wanda ya zo don neman jinyar raunin harbin bindiga.

Duk da haka daya daga ‘yan sandan mai mukamin sufeta ya rasa ran sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “‘YAN BINDIGA UKU SUN GAMU DA GAMON SU A ORLU IMO-‘YAN SANDA”
  1. You should take part in a contest for one of the highest quality
    sites online. I’m going to recommend this blog!

Leave a Reply

Your email address will not be published.