• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAKIN AMURKA A AFGHANISTAN ZAI KARE A WATAN GOBE-BIDEN

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce yakin da Amurka ke jagoranra na hana Taliban kwace madafun iko a Afghanistan zai kammala a karshen watan gobe na Agusta.

A jawabin da ya gabatar ga kasar, Biden ya ce Amurka na shirin kammala yakin da ta jagoranta na wajen shekaru 20 a Afghanistan.

Shugaban na Amurka ya nuna fargabar in Amurka ta fice daga Afghanistan zai yi wuya a samu wanzuwar gwamnati daya, don haka ya ba da shawara ga gwamnatin burnin Kabul ta nemi tattaunawa da ‘yan Taliban.

A yanzu haka Taliban ce mafi tasiri a kasar duk da dogon yakin da a ka yi da ya yi sanadiyyar zubar da jinin mutane da ba adadi.

Alamu na nuna Amurka ba ta da sauran bukata ta kakkabe wasu da ta ke dauka da ‘yan ta’adda a Afghanistan musamman bayan rayuwar Odama Ben Laden.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “YAKIN AMURKA A AFGHANISTAN ZAI KARE A WATAN GOBE-BIDEN”

Leave a Reply

Your email address will not be published.