• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAJIN AIKIN MA’AIKATAN SHARI’A A NAJERIYA NA CIGABA

Ma’aikatan kotunan Najeriya na cigaba da yajin aiki da su ka fara tun ranar 6 ga watan nan na Afrilu.

Yajin aikin sai yanda hali ya yi na bukatar cin gashin kan sashen shari’a ne ta bangaren kudi musamman a matakin jihohi.

Kungiyar gwamnoni da shugabannin majalisun dokokin jihohi sun yi zama a fadar Aso Rock don neman bakin zaren warware takaddamar.

Rokon jami’an shari’ar su dawo aiki bai yi tasiri ba don rashin cimma matsaya ga bukatar da su ka gabatar.

Yajin aikin ya kassara lamuran shari’a a Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “YAJIN AIKIN MA’AIKATAN SHARI’A A NAJERIYA NA CIGABA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *