• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAJIN AIKI-MU NA NEMAN ASUU DON WARWARE TAKADDAMA-MINISTAN ILIMI ADAMU ADAMU

ByNoblen

Feb 17, 2022

Ministan ilimi na Najeriya Adamu Adamu ya ce sun a neman kungiyar malaman jami’a ASUU don tattaunawa da su a kawo karshen yajin aikin da su ka shiga na gargadi na tsawon wata daya.
Adamu Adamu na magana ne bayan taron majalisar zartarwa da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya jaogoranta.
Ministan ya ce ya yi mamakin yanda ASUU ta shiga yajin aiki bayan warware dukkan takaddamar da ke tsakanin ta da gwamnati.
A na ta bangaren ASUU ta musanta cewa gwamnati ta nema ta da wata magana.
Yajin aikin malaman jami’a a Najeriya ya zama tamkar abun da ba za a iya kauce ma sa ba don yanda bangarorin biyu ke zargin juna da saba yarjejeniya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.