• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAJIN AIKI: A LITININ DIN NAN ‘YAN KWADAGO ZA SU AUKA YAJIN AIKI DA ZANGA-ZANGA

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC za ta auka yajin aiki da ma zanga-zanga don matsawa gwamnati lamba ta janye karin farashin fetur da lantarki da ta yi da tuni hakan ya fara tasiri a kan farashin kayan masarufi. Barazanar shiga yajin aikin na zuwa daidai lokacin da kotun kula da lamuran aikin gwamnati ta umurci kungiyar kwadago ta dakatar da matakin har sai ta gama sauraron shari’ar da gwamnati ta shigar da wata kungiya mai marawa gwamnati baya.

A taron ta na karshe a gidan kwadago da ke Abuja kungiyar kwadagon NLC da ke samun hadin kan ta kamfanoni TUC ta ce ba gudu ba ja da baya kan wannan yajin aiki har sai gwamnati ta janye tagwayen karin farashin da ta yi. Shugaban kungiyar kwadagon Ayuba Wabba ya sha nanata wahalar da ya ce ma’aikata kan shiga sakamakon karin farashin fetur. Tuni wata kungiya mai marawa janye tallafin fetur baya ta yi gangami a Abuja don gargadin sa kafar wando daya da kungiyar kwadagon ta na mai cewa ai ba yanda ma za’a dawo da tallafin na fetur. “Za mu kalubalanci ‘yan kwadagon a kotu kuma in sun fito kan titi za mu yi fito na fito da su…” Inji jagoran magoya bayan da su ka yi taro a dandalin UNITY.

Gwamnatin baya ta PDP da ta nemi cire tallafin fetur ta samu kalubalen gaske a wajen 2012 inda ala tilas ta cigaba da ba da tallafin; a lokacin wannan gwamnati na ‘yar adawa inda jama’ar ta su ka nuna lalle tallafin na da amfani. Duk da haka shugaba Buhari bai taba goyon bayan tallafin ba don a mahangar sa hakan wata hanya ce ta almundahana.

Dakatar da batun yajin aiki a kotu ba sabon abu ba ne kuma bai taba hana kungiyar kwadago daukar matakin ta ba duk da ma a na zargin ita kan ta kwadagon da zama dillaliyar gwamnati wajen kara farashin fetur tun da an ga yajin aiki bai taba sa an janye dukkan karin da a ka yi ba a baya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
8 thoughts on “YAJIN AIKI: A LITININ DIN NAN ‘YAN KWADAGO ZA SU AUKA YAJIN AIKI DA ZANGA-ZANGA”
 1. Hello there, I found your web site by the use of Google at the same time as searching for a similar matter, your site got here
  up, it appears to be like great. I’ve bookmarked it in my google bookmarks.

  Hi there, simply was alert to your blog through Google, and found that it’s really informative.

  I am gonna watch out for brussels. I will appreciate in the event
  you proceed this in future. Lots of other people might be benefited out of your writing.
  Cheers!

 2. Hey are using WordPress for your blog platform?
  I’m new to the blog world but I’m trying to get started and set up my own. Do you
  need any coding expertise to make your own blog?
  Any help would be greatly appreciated!

 3. Nice blog! Is your theme custom made or did you download it from
  somewhere? A design like yours with a few simple tweeks would really make my blog stand out.

  Please let me know where you got your design. Thanks

 4. you’re actually a excellent webmaster. The site loading speed is amazing.
  It seems that you are doing any distinctive trick. In addition, The contents are masterpiece.
  you’ve done a fantastic process on this matter!

 5. Have you ever thought about including a little bit more than just your
  articles? I mean, what you say is important and all.
  However think of if you added some great photos or video clips to give your posts more, “pop”!

  Your content is excellent but with pics and videos, this blog could certainly be one of the very best in its
  field. Wonderful blog!

Leave a Reply

Your email address will not be published.