• Fri. Sep 30th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YAHAYA BELLO YA YANKI FOM DIN TAKARAR SHUGABAN KASA A INUWAR APC

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya yanki fom din takarar shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar APC kan zunzurutun kudi Naira miliyan 100.
Bello ya zama mutum na farko a jerin masu son takara a APC da ya sayi fom din maid an karen tsada.
Daga nan ma Bello ya garzaya fadar Aso Rock inda ya nunawa shugaba Buhari fom din don sanar da shi halin da a ke ciki.
Ban da Yahaya Bello a tsakanin gwamnonin APC, a na sa ran gwamna Dave Umahi da ya sauya sheka daga PDP zai zo ya sayi fom din.
A halin yanzu dai uban siyasar APC Bola Ahmed Tinubu da ke cikin manyan ‘yan takarar na Saudiyya don gdanar umrah, inda a ke ganin da zarar ya dawo zai yanki fom din.
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ma da tuni ya fara zagawa don neman goyon baya zai karbi fom din.
Za a gudanar da zaben fidda gwani na APC a karshen watan nan na Mayu mai shigowa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
7 thoughts on “YAHAYA BELLO YA YANKI FOM DIN TAKARAR SHUGABAN KASA A INUWAR APC”
  1. I’ve read several good stuff here. Certainly worth bookmarking for revisiting. I surprise how much effort you put to make such a excellent informative website.

  2. I’m still learning from you, while I’m making my way to the top as well. I absolutely love reading all that is written on your website.Keep the information coming. I loved it!

Leave a Reply

Your email address will not be published.