• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YA ZAMA WAJIBI HOUTHI TA DAINA KAFA TARKUNAN MUGUNTA A SAN’A’A-RUNDUNAR LARABAWA

ByNoblen

Dec 29, 2021 ,

Rundunar larabawa ta yaki da ‘yan tawayen houthi a Yaman ta bukaci ‘yan tawayen su daina kafa tarkunan mugunta a babban birnin kasar San’a’a.
Rundunar ta ce houthi na kafa cibiyoyin kai hare-hare da ma amfani da filin jirgin saman farar hula wajen gudanar da aiyukan sojan tawaye.
Rundunar ta garadi houthi da ke samun goyon bayan Iran da ta kawar da cibiyoyin na ta ko kuma in ta ki ta fuskanci hare-hare ta sama.
Rundunar ta ce ta na zuba ido kan aiyukan na ‘yan houthi kuma za ta cigaba da daukar matakan hana ta miyagun laifuka bisa dokokin kasa da kasa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *