• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YA ZAMA WAJIBI DUKKAN ‘YAN AREWA SU HADA KAI DON KAWO KARSHEN KALUBALEN TSARO-MASU SHARHI

ByNasiru Adamu El-hikaya

Sep 13, 2022

Masu sharhi kan lamuran yau da kullam na karfafa kiran samun aiki na bai daya tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki na yankin arewa don kawo karshen kalubalen tsaro.

Wannan na nuna kara nuna damuwa ne kan tabarbarewar tsaro a birane, kan manyan tituna da dazuka musamman kasadar shiga gonaki don noma a tsanake.

Masu sharhin sun ce akasarin miyagun irin sanannu ne kuma ba wai sun gagari dukkan jama’a ba ne, amma rashin aiki tare tsakanin matasa, dattawa, sarakuna da sauran masana ya sanya rashin samun shawo kan matsalar.

Masanan sun ba da shawarar a samu wakilai daga dukkanin sassa su rika zama a kaduna don bitar hanyoyin magance kalubalen ta hanyar hatta amfani da wasu daga miyagun irin da su ka jingine makamai.

Hakanan sarakuna su zama su na azure daya da za su rika zama da tura sakwannin umurnin daukar matakan da su ka dace ta hanyar hakiman su zuwa har masu anguwanni da lalle hakan zai dakile fargabar da mutane ke ciki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
18 thoughts on “YA ZAMA WAJIBI DUKKAN ‘YAN AREWA SU HADA KAI DON KAWO KARSHEN KALUBALEN TSARO-MASU SHARHI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.