Mataimakin shugaban Najeiya Yemi Osinbajo ya ce ya na da muhimmanci a kula da yanda mutane ke yawa a Najeriya don daukar matakan da su ka dace.
Osinbajo na magana ne a wani babban taro da mai taimaka ma sa Maryam Uwais ta wakilce shi.
Masana na nuna ya zama wajibi a rika lura da yawan jama’a don samun damar tsare-tsare da za su iya amfana mutanen da a ka da su.
Najeriya dai na da fiye da mutum miliyan 200 inda akasarin jama’ar kasar ke rayuwa cikin mizanin talauci na samun kasa da dala daya ko ma yanzu a ce rabin dala daya wato samun kimanin Naira dari uku a wuni.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
hyweci