• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YA KAMATA SHUGABA BUHARI YA TATTARA KAN MAGOYA BAYAN SA NA AINIHI KAFIN 2023-DANMALIKIN KEBBI

Jigon siyasar APC a taraiya Alhaji Musa Abubakar Danmalikin Kebbi ya bukaci shugaba Buhari ya tattara kan magoya bayan sa na asali gabanin babban zaben 2023.
Danmalikin na magana ne kan wasu da ya zaiyana da wadanda ba su yi wata hidima a siyasar shugaban ba, amma yau su ke jagorantar lamura da rufe kofa ga wadanda su ka sha gwagwarmaya.
Dan siyasar ya ce akwai da dama daga magoya bayan shugaban da su ke yi ta faman ganawa da shi amma hakan ya gagara.
Hakanan ya nuna matukar APC na son tasiri a babban zaben, to sai ta tara magoya bayan jam’iyyun asali da su ka kafa jam’iyyar don bullo da hanyoyin sake gamsar da jama’a cewa APC za ta yi wa ‘yan kasa adalci.
Hakanan dattijon ya bukaci shugaba Buhari kar ya bari a janye dukkan tallafin man fetur don hakan zai haifar da mafi tsananin kuncin talauci.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
51 thoughts on “YA KAMATA SHUGABA BUHARI YA TATTARA KAN MAGOYA BAYAN SA NA AINIHI KAFIN 2023-DANMALIKIN KEBBI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.