• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YA KAMATA A ZAIYANA KAN IYAKA YADDA YA DACE DON KARE FITINAR KAUYUKA-SANATA BULUS AMOS

Dan majalisar dattawa daga jihar Gombe Bulus Amos ya bukaci gwamnatin taraiya ta shara kan iyaka na yankuna da jihohi dalla-dalla don kawo karshen fitinar mallakar yankuna da kan haddasa asarar rayuka.

Sanata Amos wanda ya gabatar da kuduri gaban majalisar dattawa don kai dauki ga wadanda fitinar mallakar yanki ta shafa a jihar Gombe, ya ce rashin daukar mataki a baya shi ya sa irin wannan matsalar ta ki zama tarihi.

In za a tuna al’ummar Waja  da Lunguda a jihar Gombe sun samu sabani kan filayen gonaki da hakan ya zama fitinar kabilanci har ya kai ga kashe mutum 15.

Dan majalisar na bukatar kai kayan tallafi daga gwamnati da sauran cibiyoyin ba da tallafi ga mutanen da du ka rasa matsugunan su sanadiyyar fitinar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *