• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YA DACE SHUGABANNIN SIYASA SU DAGE WAJEN KARE ‘YAN AREWA A KUDU-GWAMNA MATAWALLE

ByYusuf Yau

Apr 9, 2021

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bukaci shugabannin siyasa su dage wajen kare rayukan ‘yan arewa da a ke salwantarwa a kudu.

Gwamnan a sanarwa da ya sanyawa hannu, ya ce irin wannan batu da daga gwamnan APC zai fito, amma ya na alfahari a matsayin sa na dan jam’iyyar adawa ta PDP da baiyana wannan matsaya.

Matawallen Maradun ya ce a yanzu ran dan arewa ba shi da wata darajar karewa a yankin kudu da ya zama a na amfani da siyasa wajen aikata kisa.

Gwamnan ya bukaci daukar matakan da su ka dace wajen kawo karshen wannan mugun aiki don bukatun hadin kai da zaman lafiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *