• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WIKE YA CACCAKI OBASEKI DA NUNA MACIYIN AMANA NE

Gwamnan Rivas Nyesom Wike ya caccaki gwamnan Edo Godwin Obaseki da nuna maciyin amana ne.
Sabani ya shiga tsakanin gwamnonin biyu yayin da Obaseki ya kushe Wike da nuna ba yanda za a yi a bar shi ya yi babakere a PDP ko nuna kan sa a matsayin shi ne madugun jam’iyyar da kowa sai ya yi ma sa da’a.
Nyesom Wike ya ce zaman Obaseki a PDP tamkar zama ne a gidan haya.
Wike ya tuno cewa ai ya taimaki Obaseki a 2020 da sama masa tikitin PDP lokacin da a ka hana shi tsayawa a tsohuwar jam’iyyar sa ta APC.
A nan Wike ya nemi gafarar tsohon gwamnan jihar Adams Oshiomohle da nuna gaskiyar sa ta baiyana kan cewa Obaseki mai cin amanar wanda ya taimake shi ne.
Da alamu Wike ahi ne gwamna mafi tasiri a babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.