• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WIKE: RIBAS TA KAFA DOKAR HANA ZIRGA-ZIRGAR DARE DA MAKWABTA

Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya aiyana dokar hana zirga-zirgar dare tsakanin jihar sa da makwabta don tabarbarewar tsaro.

Dokar za ta fara aiki daga larabar nan daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe a kullum.

Ribas na da iyaka da jihar Abia, Akwa Ibom da Bayelsa.

Dokar ta biyo bayan yanda wasu ‘yan bindiga su ka hallaka jami’an ‘yan sanda, kwastam da na sibil difens a kan hanyar babban birnin jihar Fatakwal da Owerri.

A jawabi ga mutan jihar, gwamna Wike ya bukaci duk masu son shiga ko fita daga jihar su rika yin hakan kafin karfe 8 na dare kuma an tura jami’an tsaro don tabbatar da aikin dokar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *