• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WIKE NE MATSALAR PDP DUK DABYA NA DA AMFANI-MUHAMMAD HADEJA

Mataimakin kakakin PDP Kola Ologbondiyan a arewa wato Muhammad Hadeja ya ce gwamnan Ribas Nyesom Wike ne ke kawo matsala a jam’iyyar duk da ya na da amfani.

Hadeja na magana ne kan dambarwar jam’iyyar da ta haddasa murabus din mataimaka 7 a majalisar gudanarwa.

Muhammad Hadeja ya ce Wike na neman tasiri ne wajen nada jama’ar sa don zaben 2023 da hakan ya zama neman tare hanya ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ya yi wa jam’iyyar takara a 2019.

Hadeja ya ce jam’iyyar na fama da matsalar cikin gida duk da ya ce ba shi ne dalilin ficewar wasu gwamnoni daga jam’iyyar ba.

Mataimakin kakakin na adawa ya ce ya na da kwarin guiwar jam’iyyar za ta farfado ta kuma yi tasiri a 2023 musamman lokacin shugaba Buhari ke kammala mulki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “WIKE NE MATSALAR PDP DUK DABYA NA DA AMFANI-MUHAMMAD HADEJA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.