• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WATA ROKA TA ‘YAN HOUTHI TA FADA KAN WANI TITI A KASUWA A BIRNIN JAZAN

ByNoblen

Dec 8, 2021 ,

Rundunar hadin guiwar larabawa da ke yaki da ‘yan tawayen houthi a Iran ta baiyana cewa wani roka da houthi ta harba kan garin Jazan ya fada kan titi a wata kasuwar birnin.
Rundunar ta ce houthi ta sake auna yankin kudu maso yammacin Saudiyya da kai irin wadannan hare-hare a yankunan farar hula.
Rundunar ta kara da cewa houthi da ke samun goyon bayan Iran, na cigaba da watsi da dokokin duniya wajen kai farmaki kan farar hula.
A baya dai houthi kan auna filayen jiragen sama da sauran sassa na kudancin Saudiyya da ke iyaka da kasar ta Yaman.
Saudiyya ke jagorantar rundunar larabawan da ke fafutukar dawo da zababbiyar gwamnatin farar hula ta Abed Rabbo da ‘yan tawayen su ka hana zama a babbn birnin kasar Sanaa.a

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.