• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WATA ROKA DA HOUTHI TA HARBA GARIN JAZAN NA SAUDIYYA YA YI SANADIYYAR MUTUWAR MUTUM BIYU

ByNoblen

Dec 25, 2021 ,

Wata roka da ‘yan tawayen houthi a Yaman mabiya akidar shia su ka harba kan garin Jazan na kudancin Saudiyya ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu.
Makamin ya fada ne kan yankin Samtah da ke Jazan din inda dan saudiyya daya da dan Yaman daya su ka rasa ran su.
Tun farko wata rokar ta fadawa kauyen da ke makwabtaka da Najran inda ta lalata motar wani farar hula.
Rundunar larabawa ta yaki da houthi da Saudiyya ke jagoranta, ta ce an harbor makaman daga garin Saada da ke Yaman.
Rundunar ta kai hari kan cibiyoyin makamai na houthi a Saada inda ta ragargaza su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *