• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WATA FASHEWA A BIRNIN KABUL TA YI SANADIYYAR MUTUWAR MUTUM 55

Wata fashewa daf da wata makaranta a babban birnin Afghanistan, Kabul ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 55 inda fiye da mutum 150 su ka samu raunuka.

Harin dai ya faru ne daga bom da ya fashe a cikin wata mota kusa da makarantar inda akasarin wadanda su ka rasa ran su mata ne.

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya aza alhakin harin kan kungiyar Taliban.

Akasin ya rutsa da akasarin daliban mata ne don makarantar ta Sayed Al Shuhada ta raba tsarin zuwa makaranta ne kashi 3 inda a kashi na biyu mata ke daukar darasi.

An ga littattafai a watse da jakunkunan makaranta a wajen da bom din ya tashi da kuma zubewar jini.

Kakakin Taliban Zahihullah Mujahid ya ce sam Taliban ba ta da hannu a harin inda ya yi tir da harin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.