Wasu daga ‘yan majalisar zartarwar gwamnatin shugaba Buhari ta APC sun fara murabus don samun damar cimma burin sun a takarar mukamai.
Wannan kuwa cika umurnin shugaban ne na su yi murabus da hakan ya dace da tanadin sabuwar dokar zabe da za a yi amfani da ita a zaben 2023.
Hakanan an samu labarin wadanda niyyar su ba ta yi karfi ba sun fasa takarar don samun damar cigaba da zama a mukaman su.
Tuni a wasu jihohi musamman Kano masu son takara su ka ajiye mukamai don samun sukunin yin harkokin su na siyasa ba da tararradin daga bisani kotu za ta iya ture su ba don saba doka.
Gabanin umurnin nan na shugaba Buhari, masu mukaman sun yi zaman su kan mukaman da tunanin dokar ba za ta yi mu su komai ba bisa fassarar cewa hakan ya saba da tanadin tsarin mulki.