• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WASU SUNYI RUB DA CIKI KAN NAIRA MILIYAN 122 A NCC

Hukumar sadarwar Najeriya ta baiyana matakan ladabtarwa ga jami’an ta biyu da aka samu da zamba cikin aminci na tsabar kudi Naira miliyan 122.

Jami’an da su ka hada da Yakubu Gontor da Philip Eretan sun fito a rahoton jaridar yanar gizo ta Premium Times da karbar makudan kudin a dalilin alawus din tafiyar da ba su yi ba don haka karbar kudin ya zama saba doka.

Hukumar kamfanonin sadarwar NCC a takaice ba ta fadi irin ladabtarwar da ta dauka kan jami’an ba, sai dai ta tabbatar da daukar matakin ne.

NCC ta ce kwamitin ta a watan yunin bara ya samu mutanen biyu da laifin sama da fadi don haka a ka dau matakin na ladabtarwa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.