• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WASU NA AMFANI DA DALA WAJEN KARBAR CIN HANCI-EMEFIELE

ByYusuf Yau

Sep 18, 2021 ,

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya ce wasu ‘yan Najeriy na amfani da dala wajen karbar cin hanci.

Da ya ke zantawa da manema labaru, Emefiele ya ce in an zo kawo cin hanci ga wasu su kan zabi a canja kudin daga Naira zuwa Dala don kudin su zama kadan a aljihun su dadin boyewa.

Kazalika gwamnan ya zargi ‘yan canji da sayarwa wasu miyagun iri Dala su fice da ita don sayo makamai su dawo su cutar da ‘yan kasa.

Emefiele ya ce duk mai bukatar kudin ketare ya tinkari bankin sa ya ba shi kuma ko da abun da ya ke nema ya wuce ka’idar da a ka gindaya, za a tuntube su don sama ma sa kudin ya yi kasuwancin sa.

Godwin Emefiele wanda ya fara aiki tun zamanin tsohon shugaba Jonathan, ya samu dama shugaba Buhari ya sabunta ma sa wa’adi da hakan ya kawo martani da mamaki daga wadanda su ke zaton ba za a sabunta ma sa wa’adin ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “WASU NA AMFANI DA DALA WAJEN KARBAR CIN HANCI-EMEFIELE”
  1. Nice blog here! Also your web site loads up fast! What host are you
    using? Can I get your affiliate link to your host?
    I wish my website loaded up as quickly as yours lol

Leave a Reply

Your email address will not be published.