• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WASU MIYAGUN IRI NA NEMAN KIFAR DA GWAMNATIN NAJERIYA-ASO ROCK

Kakakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Femi Adeshina ya ce wasu miyagun iri daga shugabannin addini da tsoffin shugabannin siyasa na son rikita kasar ta hanyar kifar da gwamnatin dimokradiyya.

Adeshina wanda bai kira sunayen wadanda gwamnatin ke zargi ba, ya nuna wannan bisa bincike ne na sirri.

Sanarwar ta nuna wadanda ke kitsa kifar da gwamnatin na shirya amfani da kabilanci da addini wajen zuga fitinar dawowa daga rakiyar gwamnatin shugaba Buhari.

Adeshina ya ce mutanen na son cimma abun da su ka gaza cimmawa ne ta hanyar akwatin zabe a zaben 2019 da shugaba Buhari ya lashe a karo na biyu.

Adeshina ya kara da cewa gwamnatin za ta dage wajen cigaba da jagoranci har wa’adin zabe a 2023 ko da kuwa hakan zai kai ga sare fukafukan masu kumbiya-kumbiyar da laifin su na cin amanar kasa ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.