• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WASU MAZAUNA YANKIN HAKAR ZINARI A ZAMFARA SUN BA DA LABARIN AN SACE AKALLA MUTUM 40

Wasu mazauna yankin  da a ke hakar zinari a jihar Zamfara mai suna Gobirawan Chali sun ba da labarin cewa ‘yan bindiga sun shiga yankin inda su ka yi awun gaba da akalla mutum 40.
Da su ke magana ta zantawa da a ka yi da su ta wayar tarho, wasu da su ka arce zuwa Magami a karamar hukumar Maru sun ce masu satar mutanen sun so kama manyan dillalan hakar zinarin ne amma ba su tarar da su ba, don haka su ka shiga gari su ka kama talakawa ciki har da tsoffi.
Wani da ya nemi a boye sunan sa, ya ce masu satar kan nemi daga miliyan 20 a yi ta ciniki har dai a samu damar biya kafin a sako wanda a ka kama.
Mutumin ya ce wani lokacin miyagun irin kan kai ga kashe wadanda su ka kama.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.