• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WASU JIHOHIN AREWA SUN YI NA’AM DA FARFADO DA BURTALIN SHANU

Wasu jihohin arewacin arewa sun yi na’am da shirin farfado da burtalin shanu don magance arangamar manoma da makiyaya.

Tuni har wasu gwamnoni sun fara ware dazukan da za a farfado da burtalin da ke cikin dokar Najeriya da ma kungiyar rays tattalin arzikin Afurka ta yamma EKOWAS.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baiyana shirin na dawo da burtalin da gonaki, gine-gine ko wasu dalilai su ka sanya a ka kutsa cikin su har ya zama makiyaya sun rasa fitacciyar hanyar da za su rika wucewa da hakan ya sanya wasu dags ciki kan gaza wajen barin dabbobin su na barna a gonakin mutane, yayin da a ke samun wasu na yin hakan bisa ganganci.

Tun a zantawa ta musamman da gidan talabijin na ARISE shugaban ya ce ya ba da umurni ga ministan shari’a don farfado da burtalin da a ka kutsa cikin su. Burtalin kuma tun a jamhuriya ta biyu a ka tsara su. Don haka shugaban ya umurci ture duk wani shinge da a ka kafa kan burtali.

Idan wannan burtali ya yi nasara, daya daga shugabannin mata ta kungiyar makiyaya ta MIYETTI ALLAH Aisha Muhammad ta bukaci a ka dokar hana fulani mata tallar noni don hakan kan sa su shiga munanan dabi’u na fasikanci da haifar miyagun iri da ke zama wake daya tsakanin fulanin.

Tsarin dawo da burtalin ya fara daga watan jiya inda kusan jihar Binuwai ce kadai ta ki amincewa a yankin arewa, yayin da duk jihohin kudu ke adawa da tsarin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “WASU JIHOHIN AREWA SUN YI NA’AM DA FARFADO DA BURTALIN SHANU”
  1. It is in reality a nice and useful piece of information. I?¦m happy that you shared this useful info with us. Please stay us up to date like this. Thank you for sharing.

Leave a Reply

Your email address will not be published.