• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WANI TSOHON SOJAN ISRA’ILA YA BANKAWA KAN SA WUTA DON TUNO MUGGAN ABUBUWAN DA YA GANI A YAKIN GAZA

Wani tsohon sojan israila ya zubawa kan sa mai mai dangin fetur ya bankawa kan sa wuta don yanda kwakwalwar sa ta jirkita ga muggan abubuwan da ya gani a yakin Isra’ila da Palasdinawa ‘yan hamaz a Gaza.

Sojan mai suna Itzik Saidian ya tafi wajen tallafi ne inda ya zubawa kan sa mai ya cinnawa kan sa wuta da hakan ya sa ya samu mummunan kuna.

An garzaya da Saidian mai shekaru 26 asibiti da mummunan kuna a duk jikin sa.

Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya ce za su gyara yanda su ke kula da sojojin da su ka ajiye aiki.

A 2014 Israila ta gwabza yaki da ta nuna karfi marar misali kan Palasdinawa a yankin Gaza inda ta yi kisan gilla ga akasari fararen hula kimanin 2,250 inda hamas ta hallaka Yahudawa 74 da yawanci sojoji ne.

A Israila wajibi duk dan shekara 18 ya yi aikin soja. Maza kan yi shekaru biyu da wata shida inda mata kan yi shekaru biyu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *