• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WANDA YA KASHE MATA MAI NEMAN AIKI A AKWA IBOM YA AMSA LAIFIN SA

Akpan Uduak da a ka cafke da laifin kashe mai neman aiki a jihar Akwa Ibom mai suna Inigbong Umuoren ya amsa laifin sa da nuna amma ita kadai ya taba kashewa.

Bayan cafke shi, ‘yan sanda sun gabatar da shi ga manema labaru a birnin Uyo inda ya ce yaudarar Umuoren ya yi ta zo don yin aiki a gonar da a ka adana miyagun kwayoyi kuma ta amince.

Bayan ta zo ya tabbatar ma ta babu gona mai kwaya don haka gabanin ta tafi ya nemi yin lalata da ita ta amince ta hanyar sharadin amfani da kororon roba.

Uduak ya ce sanadiyyar cire kororon ya sa Umuoren ta doke shi da dutsen guga inda shi ma ya karbe dutsen ya maka ma ta ta ji rauni jini ya yi ta zuba ta mutu.

Akpan Uduak ya bunne ta a nan gidan mahaifin sa.

‘Yan sandan sun ba da tabbacin gurfanar da mai kisan gillar a gaban koto da zarar kotuna sun dawo aiki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.