• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WADANDA SU KA SACE DALIBAN GREENFIELD NA DA ALAKA DA BOKO HARAM-SHEIKH GUMMI

Dr.Ahmed Abubakar Gumi ya ce wadanda su ka sace daliban jami’ar Greenfield a Kaduna su na da alaka da Boko Haram shi ya sa su ka ki sake daliban.

Dr.Gumi na magana ne a zantawa da gudan talabijin na Channels a Kaduna.

Malamin ya ce an gano akwai alaka tsakanin barayin daliban jami’ar Greenfield da ‘yan ta’addan Boko Haram a cikin daji.

Wannan ya nuna wadanda su ka sace daliban kolejin gandun daji ta Afaka basu da alaka da ‘yan Boko Haram don sun sake daliban ba tare da kashe ko mutum daya ba; wanda ya saba da na Greenfield da su ka kashe dalibai 5.

Kazalika barayin Greenfield sun nemi diyyar Naira miliyan dari bayan karbar Naira miliyan 55 da su ka ce sun sayawa daliban abinci ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.