• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

WADANDA SU KA NEMI KIFAR DA NI SU NA NAJERIYA-INJI SHUGABA ERDONA  NA TURKIYYA

ByYusuf Yau

Oct 21, 2021

Shugaban Turkiyya Raceb Tayyeb Erdoan ya ce wadanda su ka nemi kifar da gwamnatin sa su na nan da dukiyoyin su a Najeriya.
Erdoan a jawabin sa yayin da ya kawo ziyarar aiki wuni biyu Najeriya da ganawa da shugaba Buhari, ya zaiyana wadanda ya ke zargin da cewa ‘yan ta’adda ne.
Shugaban na Turkiyya wanda ya karfafa yarjejeniyar cinikaiya tsakanin kasar da da Najeriya na biliyoyin dalar Amurka, ya bude wasu aiyuka da Turkiyya ta dauki nauyi da su ka shafi cibiyar da ta al’adun gargajiya.
In za a tuna Erdoan ya taba bukatar Najeriya ta dau matakan rufe cibiyoyin wadanda ya ke zargin da su ka hada da makarantu da asibitoci na kasaita da sauran su.
Cibiyoyin dai da ke Abuja da wasu sassa na da alaka da abokan hamaiyar Erdoan Fethullah Gulen da ke gudun hijira a Amurka tun 1999.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.