• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

UWAGIDAN GWAMNA GANDUJE TA KOMA GIDA BAYAN GAIYATAR EFCC

Uwargidan gwamnan jihar Kano Farfesa Hafsat Ganduje ta koma gida Kano bayan amsa gaiyatar hukumar yaki da cin hanci EFCC a Abuja.

Hajiya Hafsat dai ta amsa gaiyatar bayan korafin da dan ta mai suna Abdul’aziz ya rubuta kan wasu filaye da a ka sayar kuma wanda tun farko ya saya bai samu kudin sa ba.

Farfesa Hafsat Ganduje ta isa Kano ne ta jirgin sama da ya yi kama da na shata.

Kwamishinan labarun jihar Muhammad Garba ya nuna takaicin yanda wasu su ka ba da labarin da kambamawa ta hanyar nuna kama Dr.Hafsat a ka yi.

Garba ya ce Farfesa Hafsat ta dawo gida bayan amsa gaiyatar kuma har ta koma ta cigaba da aiyukan da su ka rataya a wuyan ta.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *