• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

UMAR M. SHAREEF YA ZAMA JAKADAN SABON GIDAN TALABIJIN NA QAUSAIN TV

Sabon Gidan Talabijin na Qausain ya nada Shahararren Mawaki Umar M. Shareef a matsayin jakadansa na farko a Kaduna.

Babban Shugaban Kamfanin Na Qausain Group, Alhaji Nasir Musa Idris (Albani Agege) ne ya bayyana haka a yayin kaddamarwar wanda gidan Talabijin din ya shirya a harabar ofishinsa dake Sultan Road GRA Kaduna a wannan makon.

Shugaban Kamfanin ya bayyana jin dadinsa tare da kuma mika godiyarsa ga Allah SWT da kuma ilahirin ma’aikata da wadanda suka bada gudumuwa har wannan gidan talabijin ta tabbata.

Malam Nasir ya bada tabbacin cewa gidan Talabijin din zai ta fi daidai da zamani kamar sauran manyan Gidajen Talabijin na Duniya, tare da kare dukkan wani hakkin da ya rataya a wuyansu na ganin sun samar da ingantattun bayanai da nagartaccen ilmantarwa domin amfanin al’umma bakidaya.

Shi ma a nasa jawabin Babban Daraktan Qausain, Alhaji Musa H. Isa, ya bayyana cewa sun samar da tashar Qausain TV ne daidai da zamani da kuma bin duk wasu ka’idoji na samar da ingantaccen gidan Talabijin.

Musa H Isa, ya kuma gabatar da fitattacen Mawaki Umar M Shareef a matsayin jakadan tashar ta Qausain TV.

Inda shi ma mawakin ya bayyana jin dadinsa tare da alkawarin kawo cigaba mai dorewa a matsayinsa na jakadan tashar.

Tun da farko a tsokacinsa, Babban Manajan tashar, Umar Faruk Adam ya nemi goyon baya daga al’umma da ganin sun mara wa gidan Talabijin din baya ta fuskar karfafa gwiwa da kuma kawo tallace-tallace.

Ya kuma kara da cewa sun samar da hanya mai sauki ga masu sha’awar sanya hannun jari ko son kulla alakar kasuwanci da Gidan Talabijin din na Qausain TV.

www.qausaintv.com, info@qausaintv.com
Facebook: @qausaintv, YouTube: @qausaintv, Instagram: @qausaintv

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “UMAR M. SHAREEF YA ZAMA JAKADAN SABON GIDAN TALABIJIN NA QAUSAIN TV”
  1. Pretty section of content. I just stumbled upon your weblog and in accession capital to assert that I acquire actually enjoyed account your blog posts. Any way I抣l be subscribing to your augment and even I achievement you access consistently quickly.

  2. I have discovered that service fees for online degree professionals tend to be a terrific value. Like a full College Degree in Communication with the University of Phoenix Online consists of Sixty credits at $515/credit or $30,900. Also American Intercontinental University Online provides a Bachelors of Business Administration with a overall education course element of 180 units and a price of $30,560. Online learning has made taking your college degree been so cool because you can earn the degree from the comfort of your home and when you finish from office. Thanks for all your other tips I have learned from your web site.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *