• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

UKRAINE-JIRGIN MAX YA TASHI ZUWA BUCHAREST DON KWASO DALIBAN NAJERIYA

Kamfanin jirgin sama na MAX ya ba da labarin tashin jirgin sa daya zuwa birnin Buchatrest na kasar Romania don kwaso daliban Najeriya da su ka makale a can sanadiyyar mamaye Ukraine da kasar Rasha ta yi.
In za a tuna gwamnatin Najeriya ta ware dala miliyan 8.5 don aikin wannan jigila da amfani da kamfanoni biyu da su ka hada da MAX da AIR PEACE.
Jami’in labarun kamfanin na MAX Ibrahim Dahiru ya ce jirgin na da girman da zai iya daukar fiye da fasinja 500.
Dahiru ya ce zuwa safiyar jumma’ar nan a ke sa ran dawowar jirgin don an kammala rejistar fasinjojin da zai dauko da hakan ya nuna ba a fargabar samun wani jinkiri.
Kazalika Dahiru ya ce iya aikin da a ka ba wa kamfanin na zuwa Romania ne.
Daliban da sauran ‘yan Najeriya na kasashe da ke makwabtaka da Ukraine da su ka hada da Poland, Rmania, Slovakia, Hungary har ma da wasu da su ka makale a yankin da Rasha ke da shi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.