• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

UKRAINE-GANGAR FETUR TA DAGA ZUWA SAMA DA DALA 130 YAYIN AMURKA TA HANA SHIGO DA MAN RASHA

A yanzu haka gangar man fetur ta haura dala 130 a kasuwar duniya, inda Amurka ke daukar matakan hana shigo da mai daga Rasha don zafafa takunkumi kan kasar biyo bayan mamaye Ukraine.
Man fetur din Amurka ya daga zuwa dala 126 da a ke sa ran zai gudana a watan gobe.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Amurka ta dakatar da shigowar fetur da iskar gas daga Rasha, da hakan ya nuna fetur din Rash aba zai iso tashoshin tekun Amurka ba.
Biden ya ce ya dau matakin bayan tuntubar sauran kawayen Amurka.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce kasar sa ta shiryawa duk wani takunkumi amma ba za ta yarda da bukatar da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ke son a kafa dokar hana jirage tashi a gewayen kasar sa ba.
Ga irin wannan barazana, Putin ya ce duk kasar da ta sa kan ta a wannan doka, na jan Rasha da fada ne.
Putin har sai da ya umurci masu sarrafa kunamar makaman nukiliya na kasar sa su zauna cikin shiri.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
9 thoughts on “UKRAINE-GANGAR FETUR TA DAGA ZUWA SAMA DA DALA 130 YAYIN AMURKA TA HANA SHIGO DA MAN RASHA”
 1. Thanks for the marvelous posting! I actually enjoyed reading it, you will be a great author.I will ensure that I bookmark your blog and may come back in the foreseeable future.

  I want to encourage you to continue your great work, have a
  nice holiday weekend!

 2. Thank you a bunch for sharing this with all of
  us you actually recognize what you are speaking approximately!
  Bookmarked. Please additionally visit my web site =). We may have a hyperlink trade
  contract between us

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *