• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

UBAN KASAR ZAMBIA KENNETH KAUNDA YA MUTU A SHEKARU 97

Uban kasar Zambia Mr.Kenneth Kaunda ya mutu ya na mai shekaru 97 bayan fama da jinya.

Kaunda wanda ya yi fama da masassarar sanyi, ya kwanta a asibiti a babban birnin kasar na wani dan lokaci kafin ya riga mu gidan gaskiya.

Kauda ne ya yi gwagrmayar kwatawa Zambia ‘yancin kan ta.

Kenneth Kaunda ya zama shugaban Zambia daga 1964 zuwa 1991 inda bayan faduwa zabe ya sauka daga mulki da hakan ya jawo ma sa yabo.

Tuni kasar ta aiyana kwana 21 na zaman makokin marigayin.

Kaunda ya rubuta wani littafi da ya yi suna “NOT YET UHURU” da ke nufin har yanzu ba a samu cikekken ‘yanci ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *