• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

TURKIYYA ZA TA CIGABA DA NEMAN MAN FETUR A GABASHIN TEKUN MEDIRENIYA GEFEN KASAR CYPRUS DUK DA HUSHIN TARAIYAR TURAI

ByNoblen

Sep 17, 2020 , , , ,

Shugaban Turkiyya Raceb Tayyeb Erdoan ya ce kasar sa za ta cigaba da neman mai a gabashin tekun Medeteriniya gefen kasar Cyprus.
Wannan na zuwa daidai lokacin da kungiyar taraiyar turai ke nuna hakan tsangwama ne ga makwabtan Turkiyyan.
Tuni Turkiyya ta tura jirgin hako fetur mai taken YAVUZ da rakiyan jiragen yaki na ruwa don neman man ba tareda damuwa da husatar da kasashen turai ba.
Turkiyya dai da jama’ar ta ma turawan gabar ne amma ta kasa samun yardarm sauran kasashen turai don zama memba a kungiyar taraiyar turai.
Shugaban kungiyar taraiyar turai Ursula von der ya ce duk da Turkiyya muhimmanciyar makwabciyar su ce kuma a kusa kan taswirar duniya; amma ta na dada komawa can nesa don takaddama.
Ursula van der ya ce gaskiya ne Turkiyya na yanki mai kalubale inda kuma ta ke daukar bakuncin miliyoyin ‘yan gudun hijira, amma hakan ba hujja ba ce ta cin zalin makwabtanta.
Turkiyya dai kan yi barazanar in a ka matsa ma ta lamba za ta bude iyaka ‘yan gudun hijira su bazama yankunan kasashen turai.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “TURKIYYA ZA TA CIGABA DA NEMAN MAN FETUR A GABASHIN TEKUN MEDIRENIYA GEFEN KASAR CYPRUS DUK DA HUSHIN TARAIYAR TURAI”
  1. whoah this blog is fantastic i like reading your articles.
    Stay up the good work! You realize, a lot of individuals are looking around for
    this information, you could help them greatly.

Leave a Reply

Your email address will not be published.